
Daliba a Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar kogi, Omotosho Dorcas me shekaru 26 ta rigamu gidan gaskiya a kokarin zubar da cikin gaba da fatiha da ta yi.
Lamarin ya farune a ranar 26 ga watan Augusta a Asibitin Al-Hassan Clinic and Maternity dake Lokoja.
Kafar zagazola makama tace Dorcas na dauke da cikin watanni 6 ne onda taje asibitin a zubar mata dashi wanda anan aka samu matsala ta rasu.
‘Yansanda sun je waja inda suka dauki hotuna aka kai gawarta Mutuware sannan aka kama masu hannu a lamarin.