
Wani mutum ya gamu da shanyewar rabin jiki a yayin da yake biyan bukatarsa da matar aure me ‘ya’ya 3 a dakin Otal.
Sunan Mutumin Rafiu Lasisi dan kimanin shekaru 43. Lamarin ya farune a Arigbajo Abeokuta jihar Ogun.
Sunan matar Latifat Shobowale kuma tana da aure da ‘ya’ya 3.
Hukumar ‘yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace manajan Otal dinne ya kai mata korafi inda yace mutumin yayi na farko kenan sai ya fadi kasa jikinsa ya shanye.
Hukumar ‘yansandan tace ta baiwa mutumin taimakon gaggawa kamin daga baya aka garzaya dashi zuwa Asibiti.