
Wani matashi a jihar Kano me suna Aliyu Mukhtar ya auri Budurwarsa me shekaru 16, Fatima bayan da iyayensu suka ki amincewa.
Aliyu yace ya gayawa mahaifinsa cewa zai auri Fatima amma dai mahaifin yace yayi yaro.
Dan hakane Aliyu ya je ya samu Fatima wadda itama iyayen ta basu amince ba saboda tana ajin karshe ne a sakandare aka daura musu aure.
Abokansu ne suka daura musu auren.
Duka dangin Ango da amarya sun fusata inda suka kira Hisbah suka sanar mata da halin da ake ciki dan ta yi bincike.
Hisbah ta haramta auren inda aka warwareshi saboda babu amincewar iyayen duka ma’auratan.