Friday, December 5
Shadow

Ji yanda matar aure ta mutu bayan da mijinta ya sha maganin karfin Maza yayi jìmà’ì da ita

Wata matar aure ta mutu bayan da mijinta ya sha maganin karfin maza na gargajiya yayi jima’i da ita.

Tuni dai aka gurfanar da mijin me suna Eric Katinala dan kimanin shekaru 34 inda aka zargeshi da kashe matarsa.

Lamarin ya farune a kasar Zambia.

Da yake kare kansa a Kotu, Eric yace ya koma gida daga wajan aiki sai suka fita shakatawa shi da matarsa.

yace anan ne suka sha giya kamin su bar wajan sai wata mata ta kawo maganin karfin maza inda ya siya.

Yace ko da suka koma gida matarsa ta je dafa musu abinci shi kuma sai ya sha maganin karfin mazan.

Karanta Wannan  Wahalar rayuwa a Najeriya tasa mata sun fara aikin Jari Bola

Yace bayan sun ci abinci sai suka fara saduwar aure inda a wani lokaci tace masa ta gaji.

Yace tace masa ya debo mata ruwa ta sha ya debo mata sannan tace ya zuba mata a jiki shima duk ya mata.

Yace bayan da suka huta sai suka ci gaba da jim’in.

Yace a karshe dai matarsa ta buga kanta a bango.

Yace anan ne suka tsaya suka yi bacci.

Yace da safe tace masa tana jin jiri.

Sai ya fita ya dafa musu abinci har ma dan uwanta ya je gidan suka zauna suna hira.

Yace bayan dan uwan matar ya tafi ne sai ya ji kukan dansu, ko da ya shiga gida sai ya ga matarsa kwance magashiyan.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu Me Babban Shago ta biya duka 'yan Gidansu manya da yara suka tafi aikin Umrah

Anan ne ya kira dan uwan nata suka kaita Asibiti.

Yace daga baya ta rasu.

Likitoci dai sun gano cewa akwai taruwar jini a kanta sannan akwai alamar rauni a wuyanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *