Friday, December 5
Shadow

Ji yanda Naira Tiriliyan 210 ta yi batan dabo a kamfanin mai na kasa, NNPCL

Rahotanni daga majalisar tarayya na cewa binciken yanda kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya gudanar da ayyukansa yasa an gano naira Tiriliyan 210 da suka bace.

Dan haka kwamitin dake kula da asusun ajiyar kudaden gwamnati na majalisar tarayya ya baiwa kamfanin na NNPCL kwanaki 10 ya bayar da ba’asi kan yanda aka yi da kudin.

Shugaban kwamitin, Senator Aliyu Wadada, SDP daga jihar Nasarawa ne ya bayyana hakan inda yace kamfanin na NNPCL ya nemi a bashi watanni 2 dan ya tattaro bayanai game da lamarin amma sun ki amincewa inda suka ce sun basu kwanaki 10.

Yace idan kuma basu bayar da bayanan da ake bukata ba to lallai za’a dauki mataki me tsauri akan su.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Falalar Salatil Fatih itace idan ka karantashi zaka samu ladar sauke Qur'ani daga Dubu 1 abinda yayi sama>>Inji Sheikh Abdulfatahi Sani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *