Wani sojan Najeriya me mukamin Kyaftin yayi abin yabo inda ya kubutar da kansa da wansu sauran mutane da aka yi garkuwa dasu tare.
Sojan me suna Captain J.O. Abalaka Ya kubutar da kansa ne a jihar Kogi bayan da aka yi garkuwa dashi.
Lamarin ya farune makon da ya gabata a yayin da sojan ke kan hanyar zuwa Borno inda aka mayar dashi daga Jihar Rivers inda yake aiki.
Sojan na cikin motarsa me kirar Toyota Corolla tare da karensa yayin da lamarin ya faru, saidai ya yi nasarar kwace bindigar AK47 daga hannun daya daga cikin ‘yan Bindigar inda ya kori sauran.
Sojan ya kuka kwace bindiga kirar hannu da sauran wasu abubuwa.