Monday, December 16
Shadow

Ji yanda wahalar rayuwa ta jefa kananan ‘yan mata masu shekaru 14 zuwa 16 Kàrùwàncì a Najeriya

Kananan ‘yan mata wadanda basu kammala karatun sakandare ba sun samu kansu a halin karuwanci saboda tsadar rayuwa da talauci.

A wani rahoto da jaridar Punch ta hada a Legas, wakilin jaridar ya je wani otal a Mushin inda ya nuna kamar shima ya je yin lalata da kananan yaranne.

Manajan Otal din ya hadashi da wata me suna Mayowa ‘yar kimanin shekaru 16.

Da suka ware, ya fara mata tambayoyi inda tace ta je Legas ne daga garin Ilaro na jihar Ogun.

Tace a lokacin da ta baro gida shekarunta 15 kuma dolene yasa ta bar gidan saboda iyayenta talakawa ne basa iya kula da ita, basa iya turata makaranta.

Karanta Wannan  Haziƙin Matashin Dan Asalin Jihar Katsina, Abdullahi Bature Ya Kera Mota Mai Kafa Uku, Mai Amfani Da Hasken Rana

Tace da ta je Legas ta fara yiwa wata mata aiki ne inda matar ta rika hada ta da Masu harkar kwaya.

Tace wata rana jami’an tsaro sun je wajan inda suka tarwatsa su dalili kenan da ta koma otal din take kwana inda suke biyan kudin haya Naira dubu 3 kullun, tace maza kala-kala na zuwa su kwana da ita su biyata.

Tace ita neman aiki ya kaita Legas amma da ta je sai ta tarar mata irinta ba’a daukarsu da kima a wajan.

Da aka tambayeta yaushe zata daina wannan sana’a, sai tace tana yi ne dan ta samu kudin kula da kanta amma ta shiga Adashe inda take son samun jari dan ta fara kasuwancin kanta.

Karanta Wannan  Za a fara rijistar baƙi a jihar Kano

Hakanan wakilin jaridar Punch ya kara haduwa da wata yarinya me suna Funmilayo ‘yar kimanin shekaru 17 da itama ke karuwanci a Mushin din dai.

Tace mahaifinta ya mutu ne wanda hakan yasa ta shiga wahala ta fara aikin shara a wani asibiti ana biyanta Naira Dubu 30 a matsayin Albashi wanda bai isarta ciyar da ‘yan gidansu tace daga nan ne take fita karuwanci dan samun karin kudi.

Hakanan a Yaba dake Legas itama wakilin na Punch ya gamu da wata yarinya me shekaru 15 me suna Tolani wadda tace kawartace ta kaita wajan.

Tace gidansu talakawane, su bakwai ne kuma suna kwana a matse ga yunwa, tace ba zata bari yunwa ta kashe ta ba shiyasa ta shiya wannan harka.

Karanta Wannan  Cikin Lumana Muka Yi Zaɓen 2019 Amma Aka Ƙirƙiro Mana Inkwankulusib, Céwar Ja'afar Ja'afar

Itama wata me suna A’isha ‘yar Kimanin shekaru 17 ta bayyana cewa dolene ya sa ta shiga wannan sana’a, wakilin na Punch ya sameta ne a unguwar Bariga inda tace tun tana jin tsoro har ta kai matakin da kasuwancin bai bata tsoro, tace bata son yi amma shine hanyar samun Abincinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *