
‘Yansanda a jihar Naija sun kai samame a wani otal inda suka kama mutane maza da mata ciki hadda wata matar aure.
‘Yansandan sun kai samame otal dinne bayan samun bayanan dake cewa ‘yan sara suka na amfani da otal din a matsayin mafakarsu.
Mataimakin Gwamnan jihar, Yakubu Garba ne ya bayar da umarnin kai samame maboyar ‘yan sara sukan saboda yanda suka addabi mutane.
Majiyar tace ‘yansanda basu san matar na da aure ba, sai bayan da aka fara kiran dangin wadanda aka kama, mijinta ya je ofishin ‘yansandan inda ya mata saki uku nan take.
‘Yansandan sun ce basu san abinda ya kai matar auren otal din ba dan haka zasu gudanar da bincike