
‘Yansanda a jihar Anambra sun kama wani matashi me suna Samuel Eze dan kimanin shekaru 25 da nonuwan wata mata da ya yanko.
‘Yansanda sun ce an kama wanda ake zargin a ranar Asabar,July 6, 2025 a Awada, Obosi dake jihar Anambra.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga ya bayyana cewa an kwace nonuwan matar da aka gani a hannunsa inda aka kaisu mutuware.
Yace yanzu ana kan binciken wanda ake zargin.