
Jihar Ekiti, ta haramta shan Taba a babban birnin jihar, Ado Ekiti.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Felani Oyebanji ne ya bayyana hakan a wajan zagayowar ranar yaki da shan taba ta Duniya a birnin Ado Ekiti.
Yace illar da taba kewa lafiyar dan adam ce tasa suka dauki wannan mataki.
A wani labari me kama da wannan ma, kasar Faransa ma na shirin haramta shan taba sigari.