
Wata kungiya me saka ido kan ayyukan masu ikirarin Jìhàdì me suna Nextier SPD ta bayyana cewa sojojin Najeriya 100 ne da farar hula 200 aka kashe a hare-haren masu ikirarin Jìhàdì cikin makonni 5 da suka gabata.
Kungiyar a sabon rahoton data wallafa tace akwai bukatar a sake duba ga tsarin yakar ta’addanci a Najeriya da ake dashi a yanzu.
Rahoton kungiyar yace an kai hare-hare 252 na ta’addanci a cikin watanni 6 da suka gabata sannan kungiyoyin B0K0 Hàràm da ÌŚWÀP sun kwace kananan hukumomi 3 a jihar Borno.
Kungiyar ta yi gargadin cewa ana samun karin sanyin gwiwa a tsakanin sojoji hakanan alaka tsakanin jama’ar gari da sojoji na kara yin tsami, sannan kuma hakan na nufin lamarin na iya kara kazancewa nan gaba.
Kungiyar tace rashin samun ilimi da rashin aikin yi tsakanin matasa da Talauci na kara karfafa ayyukan ta’addancin.