
Shugaba Bola Tinubu a ranar Alhamis ya yi alkawarin kare haƙƙin dimokuraɗiyya na ‘yan Najeriya na ‘yancin faɗar albarkacin baki.
A cikin jawabin Ranar Dimokuraɗiyya da ya gabatar a Majalisar Tarayya da ke Abuja, Shugaban ya ce wa jami’an tsaro kada su tsananta wa waɗanda ke sukar manufofin gwamnatinsa da ake ganin ba su yi wa jama’a daɗi ba.
“Dimokuraɗiyya na buƙatar haƙuri da kalamai masu zafi da cin mutunci,” in ji Tinubu a gaban ‘yan majalisa daga Majalisar Dattawa da ta Wakilai.
“Ku kira ni da duk sunan da kuke so, ku faɗi abin da kuke so, amma ni zan ci gaba da kira ga dimokuraɗiyya ta kare haƙƙinku na yin hakan.”
Tinubu ya shawarci magoya bayansa da ‘yan majalisa su fifita tattaunawa fiye da mulkin danniya, su fifita shawo kan juna fiye da tilastawa, da kuma kare haƙƙoƙin jama’a fiye da amfani da ƙarfi.