Wednesday, February 4
Shadow

Ka sauka daga Gwamnan jihar Delta tunda a jam’iyyar mu aka zabeka>>PDP ta gayawa Gwamna Sheriff bayan a ya koma APC, ta garzaya kotu

Jam’iyyar PDP ta yi martani kan komawar Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori zuwa jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar na riko, Ambassador Umar Damagum, ya bayyana cewa sun tafi kotu da neman Gwamna Sheriff ya sauka daa kujerar Gwamna tunda a karkashin PDP aka zabeshi.

Yace a baya sun fuskanci matsalolin da suka fi wannan yawa kuma duk sun tsallake dan haka wannan wasan yara ne.

Yace an baiwa Gwamnatin gudanarwa na yankin kudu maso kudu umarnin ya kula da jam’iyyar PDP a jihar ta Delta saboda duka ‘yan jam’iyyar a jihar sun canja sheka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon:Ta zargi cewa, Likitan mata ya nace sai ta kwanta ya duba mata jiki, saboda ya ganda da katon ciki yana tuanin ciki gareta duk da ta ce masa bata da ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *