
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, saura kiris ya daina jin labarai da karanta jaridu saboda yanda yake ganin ‘yan Najeriya a cikin wahala.
Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Katsina.
Yace amma duk da haka ya dage ya tsaya tsayin daka dan tabbatar da ganin ya dora Najeriya a turbar gaskiya.
Shugaba Tinubu yace kuma zuwa yanzu an fara ganin sakamakon matakan da ya dauka.
Inda yace lamura sun fara dawowa daidai