Tuesday, May 19
Shadow

Kaf masu neman takarar shugabancin Najeriya babu Gwani wanda ya cancanta kamar ni>>Inji Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Labour party a zaben shekarar 2027, Peter Obi ya bayyana cewa, babu Dimokradiyya a mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Ya bayyana cewa idan aka lura da abinda ya faru a jihar Rivers da zaben jihar Edo za’a iya gane cewa, babu Dimokradiyya a Najeriya.

Peter Obi ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Arise TV.

Yace shiyasa yake ta neman ya zama shugaban kasa, saboda ya gyara wannan matsalar, yace a kaf cikin masu neman takarar shugaban kasar, babu gwani wanda ke da kwarewa kamarsa saboda yayi aiki da kamfanoni kuma ya zama gwamna.

Karanta Wannan  Rikicin Sarautar Kano ya ɗauki sabon salo, inda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya naɗa wansa, Sanusi Ado Bayero, a matsayin Galadiman Kano, bayan rasuwar Abbas Sanusi. A gefe guda kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Mannir Sanusi a matsayin Galadiman Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *