Wednesday, November 19
Shadow

Wata Sabuwa: Kakakin Jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar APC

Kakakin jam’iyyar PDP a jihar Legas, Hakeem Amode ya koma jam’iyyar APC.

Ya bayyana hakane a wata ganawa da manema labarai tare da masoyansa a Ikeja ranar Litinin.

Sun bayyana cewa, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Abdul-Azeez Adediran (Jandor), da ya koma APC ne ya dauki hankulansu suka koma jam’iyyar APC.

A jawabinsa yace duka jam’iyyar PDP a jihar daga sama har kasa sun koma APC inda yace saboda jam’iyyar PDP ta tasa alkibla.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna da Duminsu Yanda Motar da su Gwamnan Katsina ta lalace bayan iftila'in fa ya fada musu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *