Wednesday, April 8
Shadow

Kai malam Shekaruna 46 ba 35 ba, kuma kai na dan Adawa ne na gaskiya ba, APC ce ta turoka ka mata Munafurci>>Nafiu Bala ya gayawa Kwankwaso

Nafiu Bala Gombe wanda ya kawo tarnaki a jam’iyyar ADC ya mayarwa da Kwankwaso zazzafan Martani inda yace Kwankwason ba dan Adawa bane na gaskiya.

Nafiu ya bayyana cewa, Kwankwaso APC ce ta turoshi ya mata munafurci a jam’iyyar ADC.

Sannan yace Shi shekarun sa 46 ba 35 ba kamar yanda Kwankwason yake fada. Sannan yace ya kamata Kwankwason yayi bincike da kyau kamin yayi magana irin waccan.

Sannan yace ko da kuwa shi yarone bai kamata Kwankwason ya rainashi ba.

Ya kara da cewa, Su Kwankwaso sun tsufa, kamata yayi su koma gefe su bar matasa su mulki Najeriya, yace kamata yayi su zama masu bayar da shawara.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Na kasa Fahimtar me nene Shugaban Kungiyar Izala, Bala Lau yace suna tare da Malam Lawal Triumph akai, Kalaman batancin da yayiwa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ko mene?>>Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana

Yace Kwankwason da sauran shuwagabannin da yawa suma a lokacinsu matasa suka fara shiga harkar siyasa.

Yace a 2023 fa Dattawan Arewa sun je suka samu Kwankwaso akan ya janyewa Atiku amma yaki, dan haka shi Munafurci yazo yiwa APC a jam’iyyar adawa ba dan adawane na gaskiya ba.

Yace dan haka bashi da damar da shima a yanzu zau tursasashi yace sai ya sauka daga shugabancin ADC musamman saboda zalincin da ake masa.

Ya gargadi Kwankwaso cewa ya bi hanyar data dace wajan shiga jam’iyyar ADC kuma ya tabbatar ya karanta dokokin jam’iyyar da kyau.

Yace shi fa bai ma kallon Kwankwaso a matsayin dan ADC dan haka bashi da damar da zai zo yace zai masa magana akan shugabancin jam’iyyar.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta samu Naira Biliyan 84 daga kudin harajin Naira 50 da take cirewa akan duk Dubu 10 da 'yan Najeriya suke fire daga Bankinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *