
Tauraruwar fina-finan Hausa, Khadija MaiNumfashi ta sanar da fitowarta daga hannun ‘yansanda bayan da aka kamata.
Tace Kabiru Legas ne ya je wajan ‘yansanda yace an yiwa rayuwarsa barazana inda aka tambayeshi wa yake zargi yace ita yake zargi.
Tace dan haka dole ne yasa aka kirata amma Allah ya wanke ta.
A karshe ta yi godiya ga masoyanta da abokan sana’arta da ‘yan uwa bisa irin soyayyar da aka nuna mata.