
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Datti Baba Ahmad, ya bayyana cewa, Kashye ‘yan Shi’a da aka yi a Zaria wanda sojoji suka yi da cewa wai sun tarewa shugaban sojoni hanya ne shiri ne.
Yace abune wanda aka shirya dan cimma wata manufa.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Ya ce kuma yana da hujjoji kan duk wani ikirari da yayi.