An kama wani dan kasar Amurka, Larry Savage saboda zargin satar kuri’a da lalata kuri’ar da cin amanar kasa.
Larry Savage dan takara majalisar tarayyar Amurka ne daa Indiana saidai bai ci zaben ba.
Lamarin ya farune a yayin da aka gudanar da zaben gwaji a Madison County dake Indiana.
An tara kuri’u ana shirin zabe sai aka ga babu guda biyu, ko da aka duba kyamara sai aka hango Larry ya saka kuri’un guda biyu cikin aljihunsa.
Larry ya sace kuri’un ne bayan samun bayanan cewa za’a iya amfani dasu a zaben gaske.
Kotu ta bada damar a binciki gidan Larry Savage inda bayan binciken aka gano kuri’un guda biyu a cikin motarsa.
Larry dai ya kai kansa ofishin ‘yansanda inda tuni aka bayar da belinsa akan Dala $500