Friday, November 8
Shadow

Gwamnati na kai mutane Bango ta hanyar kara farashin man fetur>>NLC

Kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana cewa kara farashin man fetur da gwammatin tarayya ke yi na kai mutane bango.

Kungiyar tace gwamnati ta kiyayi ranar da ran mutane zai baci su yi mata fitar ba zata.

Ta kara da cewa shirun da ‘yan Najeriya ke yi akwai randa zasu fusata idan aka kaisu bango dan kuwa ko da akuyace aka cika takura mata tana cizo.

Wani dan kungiyar ta kwadago ne ya bayyanawa kafar jaridar Vanguard haka a wata hira da aka yi dashi inda yace baya son a bayyana sunansa.

Yace matsin da gwamnati ke yi musamman na kara farashin man fetur zai kai kutane bango wanda kuma gwamnatin ce zata jawo a mata bore.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa dòn tayi kira kan mátsalar tsaròɲ garinsu

Yace idan ka cire mutanen dake cikin gwamnati da danginsu da abokansu yawanci mutane suna cikin halin yunwa da kaka nikayi.

Yace ba zai yiyu ka rika dukan yaro amma kace kada yayi kuka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *