
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri yace ya kamata a mayar da ranar Juma’a ranar hutu.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya saki a shafinsa na sada zumunta.
Yace babu adalci ace Kirista na da ranar Lahadi a matsayin ranar hutu amma ranar Juma’a ace sai an je aiki.
Yace ko dai a mayar da ranar Juma’a ranar hutu ko kuma a rage awannij da ake aiki a ranar juma’ar a rika tashi daga aiki da karfe 12 na rana.