
Wannan matashin ya yiwa Tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Nuhu tonon Silili inda yace bai tausaya mata halin da ta tsinci kanta a ciki ba.
Ya bayyana cewa, maimakon tara mata makudan kudade da mutane ke yi, kamata yayi a tambayeta abinda ta aikata, har Allah ya jarrabeta da irin rayuwar da take ciki.
Shima dai ya danganta sabon Allah da rashin yiwa iyaye biyayya musamman wajan shiga harkar fim da alaka da abinda ya samu Ummi Nuhu.