Tuesday, March 17
Shadow

Kalli Bidiyo: Bayan ya bayar da hakuri kan bidiyonsa da aka gani yana rabawa ‘yansanda kudi, An kuma kara ganin dan Chinar nan yana watsawa ma’aikatansa kudi a wajan hakar ma’adanai

Dan kasar Chinar nan da kwanakin baya aka ganshi a wani Bidiyo da ya yadu sosai yana rabawa ‘yansandan Najeriya kudi wanda har daga baya ya fito ya bada hakiri, ya sake aikata laifin.

A wannan karin, ganinsa aka yi yana watsawa ma’aikatansa kudi a kasa suna rububi a wajan hakar ma’adanai.

Wannan dai cin zarafin Naira ne kamar yanda hukumar EFCC ta Haramta yin hakan.

Abin jira a gani shine wane hukunci ne hukumomi zasu dauka a kansa.

Karanta Wannan  Duk Da rokon da 'yan majalisar Tarayya suka wa shugaba Tinubu kar a janye, Hukumar 'yansandan Najeriya ta janye 'yansanda dubu sha daya masu Baiwa manyan mutane kariya a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *