Saturday, March 15
Shadow

Kalli Bidiyo: Bill din NEPA yana cikin bashi da ake bin mutum idan ya mutum>>Inji Dr. Bashir Aliyu Al-Furqan

Babban malamin Addinin Islama, Dr. Bashir Aliyu Al-Furqan ya bayyana cewa kudin wuta da ake bin mutum bashi yana cikin bashin da ake binsa wanda kuma ya kamata a biya masa.

Malam ya bayyana hakane bayan da wasu suka aika masa Tambaya game da mahaifinsu da ya rasu inda suka ce ana binsa bashin kudin NEPA na Naira dubu dari 4.

Malam yace tabbas ya kamata a biya dan kuwa wutar mutum saya yayi ba tasa bace ba dan haka ba da saidai ya sayi Diesel ko Fetur dan ganin haske.

Malam yace ko da mutum yana tantamar kudin wutar da yake biya baya shan wutar, yace gara ya zamana kai ne kake bin bashi ba kaine ake bi ba.

Karanta Wannan  Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa

Kalli Bidiyon anan:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *