
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya kai ziyara ofishin jam’iyyar ADC a jihar Rivers.
Tun a filin jirgin sama na jihar ya fara tara mabiyansa inda suka masa rakiya zuwa ofishin jam’iyyar ADC.
A jawabinsa, yace jiharsu ta saba da rubuta sakamakon zabe ba tare da la’akari da kuri’un mutane da aka kada ba.
Yace dolene a dakatar da hakan.
Amaechi na daga cikin gamayyar ‘yan Adawa da suka fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.