
Wani matashi ya bayyana inda yace shine ya kirkiri Bidiyon AI wanda yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mutu sannan ya dora Bidiyon Shahararren me watsa labarai a Tiktok Sultan.
Hakan yasa hukumar DSS ta kama Sultan inda ta gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin Cusawa ‘yan Najeriya kiyayyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Matashin dai yace yana kira ga hukumar DSS ta saki Sultan ta kamashi.