Rahotanni daga babban birnin jihar Abia, Umahia sun bayyana cewa mayakan haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra sun kaiwa wani shingen sojojin Najeriya hari inda suka tasheshi.
Sun kai harinne a kan titin Umuahia Onuimo dake kan hanyar Imo zuwa jihar ta Abia a yau, Laraba 13 ga watan Nuwamba 2024.
Me magana da yawun sojin dake yaki a yankin kudu maso gabas, Lt. Col. Jonah Unuakhalu ya tabbatar da harin inda yace kungiyar ESN ce ta kaishi.
Yace a yayin harin, Sojojin sun tarwatsa maharan inda suka tsere suka bar motoci 2 da Lexus Jeep da kuma Sienna, saidai yace a yayin artabun, sojoji 2 sun rasa rayukansu.
Ya kuma nemi hadin kan jama’ar gari wajan ganowa da kamo maharan.
Saidai a nata bangaren,Kungiyar ta IPOB tace ta yi nasata ne a harin inda har ta nuna makaman data kwato daga hannun jami’an tsaron sojojin.