
Gobara a rumbun adana makamai a barikin soji na Giwa da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta haifar da fargaba a birnin.
Ƙarar abubuwa masu fashewa da aka ji a kwaryar Maiduguri sakamakon gobarar cikin dare da aka samu a barikin ya tada hankali, inda wasu rohotanni ke cewa harin Boko Haram ne.
To sai dai tuni mataimakin gwamnan jihar Borno Dakta Umar Usman Kadafur ya bukaci mazauna birnin da su kwantar da hankulansu tare da kasance cikin gidajensu, yayin da jami’an tsaro da ƴan kwana kwana ke aikinsu, sakamakon gobarar da ya tabbatar da aukuwar ta.
Ya kau da duk wani batu dake alakanta lamarin da harin Boko Haram.