Friday, November 6
Shadow

Kalli Bidiyo: Gobara a rumbun adana makamai a barikin soji na Giwa da ke Maiduguri ta haifar da fargaba a birnin inda makamai sukai ta fashewa mutane na ta gudun ceton rai

Gobara a rumbun adana makamai a barikin soji na Giwa da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta haifar da fargaba a birnin.

Ƙarar abubuwa masu fashewa da aka ji a kwaryar Maiduguri sakamakon gobarar cikin dare da aka samu a barikin ya tada hankali, inda wasu rohotanni ke cewa harin Boko Haram ne.

To sai dai tuni mataimakin gwamnan jihar Borno Dakta Umar Usman Kadafur ya bukaci mazauna birnin da su kwantar da hankulansu tare da kasance cikin gidajensu, yayin da jami’an tsaro da ƴan kwana kwana ke aikinsu, sakamakon gobarar da ya tabbatar da aukuwar ta.

Karanta Wannan  Bayani Dalla-Dalla: Kan halin da ake ciki tsakanin Najeriya da kasar Amurka, bayan da shugaba Tinubu ya shafawa fuskarsa toka yace Najeriya ba zata yadda a kawo matsa gagararru ba wanda suka gagari Amurka da kasarsu ta Venezuela ba
https://www.tiktok.com/@officialmannass1/video/7499257463317728518?_t=ZM-8vz52Y1ckVh&_r=1

Ya kau da duk wani batu dake alakanta lamarin da harin Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *