
Gwamnan Kano Ya Sa An Kwashe Almajiran Da Ke Kwana A Kan Titi An Kai Su Gidan Gwamnati An Ba Su Abinci Da Wajen Kwana.
A daren jiya ne dai gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gudanar da ran-gadi domin duba aikin ƙawata titin Lodge Road da gwamnatinsa ke yi inda ake sanya fulawoyi da fitilu masu amfani da hasken rana, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
A lokacin ne kuma gwamnan ya ci karo da wasu yara suna bacci a kan titin. Da aka bincika sai aka gano yara ne almajirai da ke gararamba a gari. Nan da nan gwamna ya ba da umarni a kai su gidan gwamnati su ci abinci su kwanta zuwa washe-gari a maida su hukumar Hisbah daga nan a maida su makarantarsu su miƙa su a hannun iyayensu.
Wane fata zaku yi masa?