Tuesday, November 18
Shadow

Kalli Bidiyo: Gwamnan Kano Ya Sa An Kwashe Almajiran Da Ke Kwana A Kan Titi An Kai Su Gidan Gwamnati An Ba Su Abinci Da Wajen Kwana

Gwamnan Kano Ya Sa An Kwashe Almajiran Da Ke Kwana A Kan Titi An Kai Su Gidan Gwamnati An Ba Su Abinci Da Wajen Kwana.

https://twitter.com/Sadeeq_Malo/status/1918912112694342051?t=VeplQnJIjUgsntDSyUIQzw&s=19

A daren jiya ne dai gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gudanar da ran-gadi domin duba aikin ƙawata titin Lodge Road da gwamnatinsa ke yi inda ake sanya fulawoyi da fitilu masu amfani da hasken rana, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

A lokacin ne kuma gwamnan ya ci karo da wasu yara suna bacci a kan titin. Da aka bincika sai aka gano yara ne almajirai da ke gararamba a gari. Nan da nan gwamna ya ba da umarni a kai su gidan gwamnati su ci abinci su kwanta zuwa washe-gari a maida su hukumar Hisbah daga nan a maida su makarantarsu su miƙa su a hannun iyayensu.

Karanta Wannan  Mijinta ya kamata tana yiwa dan kishiyarta me shekaru 15 fyade, saidai duk da haka ta sake kiran yaron inda take tambayarshi ta gamsar dashi kuwa?

Wane fata zaku yi masa?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *