
An hango diyar tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari, watau Zahara Buhari tana ta tsala kuka a kofar Asibitin da mahaifin nata ya rasu a landan.
An kuma hango dan uwanta, Yusuf Buhari na bata hakuri.
Tuni dai aka yi shirin dawo da gawar shugaba Buhari Daura dan yi masa Sallah a kuma binneshi.