
Masu son kafa kasar Biafra sun nuna Gwamnoni 40 na kasar tasu da suke son kafawa.
An ga bidiyon yanda suke nuna Gwamnonin a kafafen sada zumunta yana yaduwa sosai.
Shuwagabannin kungiyar biyu watau Nnamdi Kanu da Simon Ekpa duka suna hannu inda hukumomi ke zarginsu da aikata laifuka daban-daban.