Friday, January 16
Shadow

Kalli Bidiyo: Ni Har Ka’aba an je an tsine min Albarka kuma babu abinda ya sameni, dan haka masu kusheni saboda an daukeni hoto da Wayar dubu 13 babu abinda zai sameni>>Inii Gfresh Al-amin

Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, har Dakin Allah, Ka’aba an je an tsine masa dan haka babu abinda zai sameshi.

Ya bayyana hakane a sabon Bidiyon da ya saki inda yake mayar da martani game da hotunanda da aka dauka a wajan wani biki daya halarta.

An ga Gfresh da kuraje cike da fuskarsa, ba kamar yanda aka saba ganinsa fuska fresh ba kamar ta jarirai a Bidiyonsa.

Gfresh yace an mamayesu shi da Murja Kunya an yi amfani da wayoyi masu arha aka daukesu hotuna, yace dan haka shi ya fara tunanin kara tsaro a kusa dashi.

Yace kuma babu abinda zai sameshi dan mai abinda yafi haka bai kunyata ba.

Karanta Wannan  Bariki ba dadi, Gidan iyaye yafi dadi, Dan Allah ku daina zagin mu, ku rika mana Addu'a mu da muka fito daga gidan iyayen mu muka shiga bariki, Allah ya shiryemu>>Inji A'isha Beauty
https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7545934313934605575?_t=ZS-8zWMycKyQbJ&_r=1
https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7546308686071745799?_t=ZS-8zWNVcH6tO5&_r=1

Gfresh yace an mayar dashi wani Salmanu, amma yace duk da haka kaf ‘yan fim da mawaka babu wanda zai iya tara jama’ar da zai tara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *