
Shugaban masu garkuwa da mutane na jihar Zamfara, Bello Turji ya bayyana cewa, ba gaskiya bane ikirarin da wani me suna Musa yayi na cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ne ke daukar nauyinsu.
Bello Turji yace Shi kansa ya tsani Karamin Ministan dan a zamaninsa ne aka kashe mutu mutane sama da 70 dan haka tsakaninsa dashi saidai Allah.
Yace amma shi abinda yasa ya fito yayi magana shine ba zai yadda a yi amfani ko a hada kai dashi a batawa wani suna ba, yace au daga Allah ne babu wani me daukar nauyinsu.