
Wasan Mari da mafi yawanci ake ganin Turawa na yi ya shigo Najeriya.
Wasan wanda har ana saka kyauta ga wanda yafi iya yin marin an ganshi an fara yinshi a Najeriya.
Lamarin dai ya baiwa mutane mamaki sosai inda ake ta muhawara akai.
Tuni dai wani malamin Addinin Islama ya jawo hankalin Musulmai da cewa wasan bai halasta ba a Musulunci kuma su gujeshi.