Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Edo, Monday Okpebholo yayi subul da baka inda yace zasu kawowa jihar matsalar tsaro.
Ya bayyana hakane a yayin yakin neman zabe.
Saidai duk da cewa bisa kuskurene yayi wannan magana, lamarin ya jawo cece-kuce musamman a kafafen sada zumunta.