
Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa, da gaskene, Wasu matuka jirgin sama a Najeriya suna shaye-shayen wiwi.
Yace wasu lokutan sai ya hau jirgi idan ya ga yanayin Matukin sai ya sauka saboda tsaro.
Sanata Kalu ya zargi hukumomin dake kula da matuka jirgin da sakaci wajan kula da cewa basa shaye-shaye kamin su hau jirgi su tuka.
Ya kuma bukaci a kula da titin da jirgin ke sauka wanda yace yana bukatar gyara.
A kwanakin baya dai, An samu wani Matukin jirgin sama da Shan wiwi a Najeriya.