
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, farashin kayan abincin ya sauka saboda tsare-tsaren gwamnatinsa.
Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Daniel Bwala a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na AriseTV.
Ya kara da cewa, idan aka kwatanta yanda Najeriya take a yanzu da yanda take kamin shugaba Tinubu ya hau mulki za’a ga banbanci.
Ya koka da cewa kasafin kudin Najeriya duka bai wuce dala Biliyan $30 ba sannan ga asibitoci a lalace ga tituna a lalace da sauransu.
A karshe dai ya tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya sauka.