Wani tsohon bidiyon haduwar Shugaban kasa, Bola Ahmad da shugaban jam’iyyar APC, Dr. Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana a shafukan sada sumunta.
A bidiyon, an ga wani matashi wanda aka bayyana da cewa, dan tsohon gwamnan Kanon ne, Ganduje wanda ya gaisa da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Saidai yanayin gaisawar tasu ta jawo cece kuce saboda bai durkusa ba hannu kawai ya bashi suka gaisa.
A al’adar yarbawa dai har kwanciya ana yi wajan gaishe da manya.