Thursday, March 19
Shadow

Kalli Bidiyon: Abinda Sarkin Ingila ya gayawa shugaba Tinubu da ya dauki hankula sosai

Sarkin Ingila, King Charles ya gayawa shugaba Tinubu, Naija No dey carry last.

Lamarin ya dauki hankula sosai inda akai ta tafi.

Wannan turancin ‘yan Najeriya ne dake nufin ba’a barin Najeriya a baya.

Sarki Charles ya bayyana hakane a karshen jawabin da yayi a wajan taron cin abinci na girmamawa da aka shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a Ingila.

Shugaba Tinubu dai na ziyarar aiki a Ingila irin ta ta farko da wani shugaban Najeriya yayi a cikin shekaru 37 da suka gabata.

Karanta Wannan  Karanta Abubuwa 10 da 'yan Najeriya suka fi kashe kudinsu akai yayin da ake cikin matsin rayuwa

Ana sa ran wannan ziyarar aiki zata jawo hankalin Ingila ta zuba jari a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *