Sunday, December 28
Shadow

Kalli Bidiyon: Bangaren Aminu Saira sun yi karin hasken kan haska shirin Labarina duk da rasuwar Fulani

A yayin da cece-kuce suka yi yawa akan haska shirin labarina duk da rasuwar daya daga cikin jaruman fim din watau, Fulani, Bangaren Me shirya fim din, Malam Aminu Saura sun yi karin Haske.

Ahmad Nagudu wanda daya ne daga cikin na kusa da Malam Aminu Saira yace ya je jana’izar Fulani ba kamar yanda ake cewa babu wanda ya halarci jana’izar marigayiyar ba.

Yace kuma shirin Labarina tun ranar Laraba aka dorashi.

Yace kuma akwai kamfanoni da suka riga suka bayar da talla

Yace kuma Aminu Saira yayi kokarin a dakatar da fim din ama abu ya gagara.

Karanta Wannan  Baka da Tarbiyya>>El-Rufai ya mayarwa da Reno Omokri martani bayan da ya zargeshi da zagin Annabi Isa(AS)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *