Tuesday, May 19
Shadow

Kalli Bidiyon da Duminsa: Shugaban kasa, ji abinda ya faru da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bayan da yayi Tuntube ya fadi a kasar Turkiyya

Biyo bayan Tuntuben da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi ya fadi a kasar Turkiyya, yayin da yake tafiya shi da shugaban kasar Turkiyyan Recep Erdogan.

Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa, shugaba Tinubu yana cikin koshin Lafiya.

Sanarwar wadda ta fito daga bakin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa, yanayin yanda aka shimfida kafet din da shugaba Tinubu ke tafiya akai ne bai shimfidu da kyau ba shiyasa yayi Tuntuben.

Sanarwar tace shugaba Tinubu bai ji ciwo a faduwar da yayi ba, kuma yanzu haka ya ci gaba da ziyarar aikin da yake a kasar ta Turkiyya.

Karanta Wannan  Bayan na Farko, Matatar Man fetur din Dangote ta sake aika Jiragen Ruwa uku dauke da Gas zuwa kasar Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *