
Dan gidan Tsohon Gwamna Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai me suna Ibrahim El-Rufai ya dauki Hankula sosai a kafafen sada zumunta bayan ganinsa da kitso da Dankunne.
Ya bayyana cewa yana kuma saka Sarqa da Barimar Hanci.
A Bidiyon da ya saki a shafinsa yace bashi da wata alaqa da mutanen Arewa dan haka su fita a rayuwarsa su daina bibiyarsa a shafin sa na sada zumunta.

Da yawa da sun yi mamakin ace El-Rufai na da fandararren da irin wannan inda wasu ke cewa yawanci Duk ‘yan siyasar Najeriya na da akalla da daya da ya fandare musu inda ake kawo misalin Gwamnan Anambra, Soludo da kuma Peter Obi wadanda sukansu ke zargin ‘ya’yansu ‘yan Luwadi ne.