Friday, December 26
Shadow

Kalli Bidiyon Dansanda cikin Dariya yana cewa, ‘yan Mata ‘yan Makarantar Jihar Kebbi na cikin Tasku dan kuwa kullun sai An aikata Alfasha dasu, Yanzu haka ma duk sun dauki ciki

Wani Dansandan Najeriya ya dauki hankula bayan da aka ga Bidiyonsa yana fadar kalaman da basu dace ba akan ‘yan mata ‘yan makarantar jihar Kebbi da aka yi garkuwa dasu.

An gan shi a wajan wani cin Abinci inda yake cewa Allah ya tsareshi kada a aikashi ya kubutar da ‘yan matan.

Sannan yace kullun ne sai ‘yan Bindigar sun aikata alfasha da ‘yan matan, yanzu haka ma duk sun dauki ciki.

Wannan kalamai nasa dai sun jawo cece-kuce inda da yawa ke Allah wadai da abinda ya fada wasu ma na kiran a koreshi daga aiki.

Da yawa sun bayyana cewa, Abin kunya ne irin wadannan kalamai na fitowa daga jami’in tsaro.

Karanta Wannan  NNPCL ya fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna
https://twitter.com/AsakyGRN/status/1991998539740893634?t=b6I3FfCOsWEMIBlfJrQu6Q&s=19

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *