Friday, January 16
Shadow

Kalli Bidiyon lokacin da Samha M. Inuwa ta bayar da kyautar dalar Amurka 100 wanda tace shine ya tsonewa wasu idanu har suka mata Asiri ta yi Haddarin mota a hanyarta ta komawa Kano daga Kaduna

A wajan Bikin Dan Kannywood, Jamilu Adamu Kochila wanda aka yi a Kaduna, Samha M. Inuwa ta bayar da kyautar Dalar Amurka 100.

An ga yanda Samha ke rawa inda ta ciro dala 100 a jakarta ta mikawa wani kyauta.

A hanyarta ta dawowa gida Kano, daga Kaduna, An ga yanda Samha ta yi mummunan hadarin mota wanda motar tasu ta daki bayan Tirela.

A Bidiyon Samha da aka gani bayan Hadarin, Tace Jifa ce aka mata daga kawai ta yi kyautar Dala $100. Samha tace Addu’ar Iyaye ce ta tseratar da ita.

Saidai Samha tace ba zata daina kyauta ba duk da abinda aka mata.

Karanta Wannan  Labari ne cike da Darasi: Ji irin whulakanchin akawa Sabon Shugaban sojojin Ruwa da shugaba Tinubu ya nada Rear Admiral Idi Abbas a mahaifarsa ta garin Jos a lokacin yana kokarin shiga aikin soja
https://vt.tiktok.com/ZSSmmJgHC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *