
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, Akwai fatawowi akan shugabancin mace.
Yace akwai malaman da suka ce kwata-kwata mace ba zata yi shugabanci ba, akwai wanda suka ce zata iya yin shugabanci a wasu kebantattun gurare
Sannan Akwai wanda suka yadda zata iya yin kowane shugabanci.
Malam yace shi a na tsakiya yake, kuma ba zai daina bayyana fatawar da ya yadda da ita ba.
Malam ya bayyana hakane bayan sukar da ake masa biyo bayan fatawar da ya baiwa wata mata cewa zata iya yin shugabanci