
Malaman Darika da yawa ne suke sukar malam Lawal Triumph bayan da ya karanto Adisin dake cewa an samu Kwarkwata akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Malaman darikar dai sun bayyana wannan da cewa cin fuska ne da rashin ganin darajar Annabi(Sallallahu Alaihi wasallam).
Sannan sun ce Ko da an ruwaito wannan Hadisi bai kamata a rika karantashi ba dan bai dace da Annabi(Sallallahu Alaihi wasallam) ba.
Saidai an samu wasu malaman Izala da suka fito suke kare malam Lawal Triumph.