
Dan gidan babban malamin addinin Islama, Sheikh Khalifa Sani Zaria da aka kama bisa cewa an bashi kudi yayi addu’a ya magantu.
A hirar da RFI Hausa suka yi dashi, yace sun yadda za’a mayarwa da gwamnati kudin da ake zargin an baiwa Malam dan yayi addu’a.
Yace sun yi magana sau daya da malam tun bayan da aka tafi dashi kuma ya bayyana musu cewa lafiyarsa qalau.